IQNA

Martanin kungiyar sa ido ta cibiyar Al-Azhar kan wata shubuha  game da kur’ani

14:15 - April 07, 2024
Lambar Labari: 3490947
IQNA - Kungiyar Al-Azhar ta kasar Masar ta mayar da martani ga wata shubuha game da darajar saukar Suratul Tawba.

Shafin sadarwa na yanar gizo na Alkahira 24 ya habarta cewa, Dr. Raham Abdallah babban darektan cibiyar yaki da tsattsauran ra’ayin addini ta Al-Azhar ya mayar da martani ga wata shubuha  dangane da darajar saukar suratu Tawba a cikin kur’ani mai tsarki.

Raham Abdullah ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin a ranar Juma’a 17 ga watan Afirilu, inda yace babu wata sura ko aya mafi hatsari a cikin Alkur’ani mai girma, domin Ubangijinmu ya ce Alkur’ani haske ne, kuma an saukar da shi ne domin shiryar da dan Adam kuma shi ne mai shiryarwa tunatarwa da waraka ga duniya, haka nan kuma Ubangiji ya saukar da shi domin ya fitar da mutane daga duhu zuwa ga haske.

Ya kara da cewa: Wasu suna yada jita-jita da shakku don tsoratar da wasu daga kur'ani. Daya daga cikin wadannan jita-jita ita ce, suna cewa Suratul Tawba ta sauka ne a cikin yanayi mai hadari bayan yakin Tabuka, kuma a lokacin ne Rumawa suka baiwa runduna masu yawan gaske domin ruguza hukumar da Manzon Allah (SAW) .

Wasu kabilun larabawa maimakon su kare kasarsu sai suka karya alkawarin da suka yi da Annabi (SAW). Ana cikin haka ne aka saukar da surar tawba wadda ta tozarta wadannan munafukai.

Ya kara da cewa: Wannan sura ta sauka ne a kan uzurin mutanen da ba za su iya shiga yaki da Annabi (SAW) ba. Bayan ya fadi haka, ya ce ina hadarin wannan sura?

 

4208934

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kur’ani sura annabi uzuri manzon allah (saw)
captcha